Safarar giwaye na barazana ga rayuwar su

Giwaye a Thailand Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Giwaye a Thailand

Wani rahoto ya ce, a yayinda suke kokarin koma shiga safarar dabbobi mai tsoka, masu fasa-kwourin giwayen suna tsare da su ne a wani kuntataccen yanayi a Myanmar.

Rahoton ya yi ikirarin cewa giwayen wadanda akasarinsu matasa ne ana wulakanta su, yayinda ake tsokanarsu saboda jan hankalin masu yawon bude ido a sansanoni a Thailand.

Masu fafutukar ganin an daina safarar giwayen suna fargabar karuwar fasa-kwourinsu zai iya yin barazana ga rayuwar dabbobin a Myanmar da ake kira Burma.

Suna kira ga gwamnatin kasar Thailand ta gaggauta tsaurara dokoki na safarar giwayen.

Nazarin wanda Kungiyar dake sa ido kan dabbobin daji ta hada ya ce, an kame kimanin giwaye 81 ta haramtacciyar hanya don sayar da su a masana'antar yawon bude ido ta Thailand a tsakanin shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2013.

Dr Chris Shepherd yace "idan ka kama giwa, ka yi ma ta dukan da ya ratsa ta, har ta yi zallo, to ka samu giwar wasa".

Ana amfani da dabbobin ne akasari don jan hankalin masu yawon bude ido na cikin gida da na kasashen waje.

Saboda masu ziyara sun fi nuna sha'awar ganin kananan giwayen, farashinsu ya yi tashin gwouron-zabi. Kudinsu a yanzu ya kai dola dubu 33, ga giwa mai koshin lafiya.

A wani samame da hukumomin Thailand suka kai a shekara ta 2012, an yi nasarar hana mafi rinjayen huddar cinikin daga Myanmar.

Sai dai kuma a cewar masu fafutukar ganin an daina safara giwayen, an cigaba da tarkon giwayen, saboda masu fasa kwourinsu sun yi imanin cewa za a kawo karshen samamen da ake kaiwa na kame masu safara su.

Karin bayani