Australia: An soke harajin gurbataccen hayaki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Labor ce ta kirkiro da harajin ga kamfanoni masu fitar da gurbataccen hayaki

Majalisar dattawan Australia ta kada kuri'ar soke harajin da gwamnatin Labor ta sanya na fitar da gurbataccen hayaki akan manyan masu gurbata muhalli

Firai Minista Tony Abbott wanda gamayyar jami'iyyarsa ta doke Labor a zaben bara ya dauki soke harajin abu mai mahimmanci da gwamnatinsa zata yi.

'Yan siyasa sun yi ta tayar da jijiyar wuya game da wannan haraji tsawon shekaru.

Labor dai ta ce harajin zai taimaka wajen dakile canjin yanayi amma jam'iyyar Liberal ta yi ikirarin cewa harajin yana kawo cikas ga harkokin kasuwanci

'Yan Majalisar dattawan Australiyan 39 ne suka kada kuri'ar soke harajin.

An kirkiro da harajin a watan Yulin shekarar 2012 kuma ana cazar manyan masu gurbata muhalli su 348, £13 ga duk tan daya na gurbataccen hayakin da suke fitarwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu sukar harajin sun ce harajin na sa farashin makamashi ya tashi ala tilas

Masu sukar harajin dai da suka hada da Mr Abbott,sun ce harajin na haifar da rashin ayyuka da kuma sa farashin makamashi ya tashi ala tilas.

An gudanar da zanga zangar kin jinin kirkiro da harajin a Australia kuma soke harajin yanzu wani babban bangare ne na irin alkawarun zaben da Mr Abbot ya dauka.

Firai Minista Tony Abbot ya ce harajin gurbataccen hayakin ba shi da amfani.

Don haka Firai Ministan ya bayyana matakin soke harajin da cewa wani labari ne mai dadin ji ga iyalai a Australia kuma yana fatan maye gurbinsa da wani tsari daban wanda zai taimakawa masana'antu wajen rage gurbataccen hayakin da suke fitarwa

Jamiyyar Labor da ta Greens sun kada kuri'ar kin amincewa da soke harajin inda shugabar jam'iyyar Greens Christine Milne ta bayyana kuri'ar da aka kada ta soke harajin a matsayin wata rana mara dadi a Australia.

Jam'iyyar Labor ta zargi Mr Abbott da maida kasar baya yayinda sauran kasashen duniya ke yin gaba.