Fulani sun zargi sojoji da kona musu gidaje

Image caption Wasu daga cikin dakarun Nigeria

Fulani a yankin kudancin jihar Kaduna na zargin sojojin Nigeria da kaddamar da hare-hare a kansu babu gaira babu dalili.

A cewar Fulanin sojoji sun kona musu gidaje 35 tare da harbe musu mutane uku a karamar hukumar Jama'a.

Rundunar sojin kasar a martanin da ta mayar ta ce ba dabi'ar soji ba ce kai hari ga wanda bai da wani laifi.

Kudancin jihar Kaduna na fama da rikici mai nasaba da addinni da kabilanci a cikin 'yan shekarun nan.

Fararen hula sun dade suna zargin jami'an tsaron Nigeria da cin zarafinsu amma sojojin suna musantawa.

Karin bayani