'Yan bindiga sun sace 'yan kasuwa a Gamboru

Image caption 'Yan Boko Haram sun kashe fiye da mutane 200 a garin na Gamboru a wani harin da suka kai a baya

Rahotanni daga garin Gamboru Ngala na cewa wasu 'yan bindiga sun shiga garin inda suka yi awon gaba da wasu 'yan kasuwa biyu.

Kafin harin na maraicen ranar Laraba, kungiyar Boko Haram ta sha ikirarin kai hare-hare a garin na Gamboru da ke jihar Borno a Najeriya.

Kuma mazauna garin sun ce a baya-bayan nan ana ta kai hare-haren dauki dai-dai a yankin da kewayensa.

Wani mazaunin garin dai ya ce suna zaune ne cikin fargaba.