Hollande zai gana da Mahamadou Issoufou

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabannin biyu za su tattauna yarjejeniyar kamfanin Areva da tsaro da kuma tattalin arziki.

A Jamhuriyar Nijar yau ne Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande ke kai wata ziyara ta yini daya a Yamai inda zai gana da takwaransa na Nijar din Alhaji Mahamadou Issoufou.

Ziyarar Shugaban Faransan a Yamai wani bangare ne na karfafa dankon zumuncin dake akwai tsakanin kasashen biyu.

Maganar tattalin arziki da tsaro da yarjejeniya da kamfanin Areva na daga cikin batutuwan da shugabannin kasashen biyu za su yi magana a kai.

Shugaban na Faransa zai kuma ziyarci sansanin sojojin kasarsa da ke birnin Yamai kafin a karshe ya jagoranci taron manema labarai.

Masu sharhi sun soma tofa albarkacin bakinsu game da wannan ziyara.