'A sauya mana kwamishinonin 'Yan Sanda'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dattawan Ibo na bukatar a kwashe kwamishinonin 'Yan sanda 'yan asalin arewa daga yankin su

A Najeriya, wata kungiyar dattawan kabilar Ibo ta kudu maso gabashin kasar, wadda a Turance ake kira 'Igbo Leaders of Thought' ta yi kira da a hanzarta sauyawa kwamishinonin 'yan sandan jihohi biyar na shiyyar kudu maso gabashin Najeriyar wuraren aiki.

Kungiyar ta yi wannan kira ne bisa la'akari da cewar, yankin yana fuskantar barazanar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram, ga shi kuma tace dukkanin Kwamishinonin 'yan sandan yankin mutanen arewacin kasar ne, kuma musulmi Hausawa ko kuma Fulani.

A don haka kungiyar take neman a sauya su, ko kuma a gauraya su da nasu jami'an 'yan sandan.

Kungiyar dattawan ta ce tana son a dauki wannan mataki ne saboda barazanar da Shugaban Kungiyar Boko Haram ya yi na cewa zasu kaddamar da hare hare a yankin kudancin Kasar.

Sai dai wasu masu lura da al'amuran yau da kullum a arewacin Najeriyar sun soki wannan kira da kungiyar dattawan Ibon ta yi, suna masu cewa abin bakinciki ne wanda kuma ke neman janyo wata fitina.