Isra'ila da Hamas sun cimma tsagaita wuta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kowanne bangare ya ce zai dakatar da bude wuta

Kungiyar Hamas ta Palasdinawa da kuma Isra'ila sun amince za su girmama wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'oi biyar a Gaza a yau.

Tsagaita wutar ne zuwa ne bayan shafe kwanaki 9 suna gwabza fada.

Rundunar Sojan Isra'ila ta ce za ta dakatar da kai hari daga karfe goma na safiya don baiwa mazauna Gaza damar neman muhimman kayan bukatun rayuwa.

Wani kakakin Hamas Sami Abu Zukhri ya tabbatar da cewa kungiyarsa ma za ta dakatar da harba rokoki a wannan lokacin.

An kashe Palasdinawa sama da 200 a rikicin da kuma dan Isra'ila mutum guda.