An kai hari a birnin Kabul na Afghanistan

Hari a Afghanistan Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Hari a Afghanistan

'Yan sanda a Kasar Afghanistan sun yi musayar wuta da masu tayar da kayar baya a kusa da filin jirgin saman Kabul.

An ce 'yan tawayen sun rinka harba makaman roka ne kan filin jirgin saman daga cikin wasu gine-gine ne da ba a amfani da su.

An ba da rahotannin karar bindigogi da fashewar wasu abubuwa daga lokaci zuwa lokaci da kuma wani hayaki dake tasowa daga filin jirgin saman da kungiyar tsaro ta NATO da jirage na farar hula ke amfani da shi.

Wani mai magana da yawun 'yan sandan Kabul ya ce, ba a da masaniyar yawan masu tada kayar-bayar dake kai harin.

Babu dai wasu rahotanni da aka bayar na mutanen da suka jikkata. Kungiyar Taliban ta ce ita ce ta kai harin.

Karin bayani