Jirgin saman Malaysia ya fadi a Ukraine

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Duka fasinjojin cikin jirgin sun mutu

Jirgin saman Malaysia dauke da fasinjoji 295 wanda ya taso daga Amsterdam zuwa Kuala Lumpur ya fadi a Ukraine kusa da kan iyakar kasar da Rasha.

Kamfanin jirgin Malaysia ya ce jirgin kirar Boeing 777 ya yi batan-dabo lokacin da ya shiga sararin samaniyar kasar Ukraine.

Yankin da jirgin ya fadi, yanki ne da 'yan tawaye 'yan aware masu goyon bayan Rasha ke fada da dakarun gwamnatin Ukraine.

Rahotannin da ba a tabbatar ba sun ce an harbo jirgin saman ne da makami mai lunzami.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce wani wakilinsa ya ga jirgin a kasa ya na ci da wuta ga kuma gawarwaki watse a kasa.

Karin bayani