Boko Haram: An kashe malamai 176

Image caption Gwamna Shettima ya koka game da rikicin Boko Haram

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce an kashe malaman makaranta 176 tare da kona makarantu fiye da 900 tun lokacin da aka soma rikicin Boko Haram a shekara ta 2011.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron kwamitin kokarin samar da kariya a makarantun kasar.

Tsohon Firai Ministan Birtaniya, Gordon Brown ne a kan gaba a shirin samar da kariya ga makarantun.

Rikicin Boko Haram kuma ya raba mutane fiye da dubu 600 da muhallansu, yayin da a wannan shekarar kadai aka kashe mutane fiye da 3,000.

'Yan Boko Haram na adawa da karatun Boko abin da ya sa kungiyar ta sace dalibai 'yan mata fiye da 200 a cikin watan Afrilu a makarantarsu da ke Chibok.