Hollande ya kare ziyarar Afrika ta yamma

Image caption Shugaba Hollande na Faransa a Afrika

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya kammala ziyarar kwanaki uku da ya kai yammacin Afirka da ziyara a Ndjamena babban birnin kasar Chadi wadda ke zama cibiyar sabuwar rundunar sojin Faransa da za su gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a yankin.

Za'a tura sojoji dubu uku a fadin Sahel da kuma yankin kudu da hamadar Sahara a kokarin shawo kan rikice rikice a yankin.

Rundunar za ta maye gurbin sojojin Faransa a Mali wadanda ke taimakawa wajen kakkabe mayaka masu kishin Islama da sauran yan tawaye.

Bugu da kari Faransar tana da sojoji kimanin dubu biyu a jamhuriyar tsakiyar Afirka.

Tun farko a ziyarar tasa a Nijar Shugaban ya gana da takwaransa na Niger Mohammadu Issoufou inda suka tattauna akan yadda za a inganta tsaro a yankin sahel da rage talauci da kuma gibin da ke akwai ta fanin jin dadin rayuwa tsakanin jinsuna.

Faransar ta kuma tallafawa Niger da kudade miliyan euro miliyan 75 domin inganta ayyukan ilmi da kiwon lafiya da ginin dam din Kandaji domin samar da abinci ta hanyar bunkasa ayyukan noma da samar da makamashi da kuma wasu ayyukan.

Shugaba Issoufou ya kuma yi kira ga kamfanonin Kasar Faransa da su shigo Nijar domin su saka jarinsu.

Francois Hollande na Faransa ya kuma yi alkawarin dafawa kasashen yankin sahel wajen magance matsalar tsaro

Kowanne bangare dai ya nuna gamsuwarsa game da yadda huldar kasashen biyu take tafiya a lokacin ziyarar.