Fyade: Iyaye sun ki kai yara makaranta a Indiya

Image caption Matsalar fyade ta zama ruwan dare a Indiya

Iyaye sun fara kauracewa wata babbar makaranta da ke birnin Bangalore a Indiya, bayan zargin yi wa wata yarinya 'yar shekaru shida fyade.

Ajujuwa dai sun kasance babu dalibai a ranar Juma'a, yayin da iyaye ke cewa ba za su bar 'ya'yansu su dawo makarantar ba har sai an amince da wasu bukatu na tabbatar da kariya ga yaransu.

'Yan sanda sun ce suna bincike game da zargin da ake yi wa wasu malaman makarantar biyu, amma kawo yanzu ba a kama kowa ba.

An yi wa yarinyar fyade ne kusan makonni biyu da suka wuce, amma lamarin bai bayyana ba sai bayan da likita ya duba ta saboda rashin lafiya.

Karin bayani