Lauyoyin arewa sun bukaci tantance 'yan kudu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wata kungiyar Ibo ta nemi a sauya kwamishinoni 'yan arewa da ke kudu-maso-gabashin Najeriya

Wata kungiya ta wasu 'yan arewacin Nigeria ta kirkiro wani kudurin doka da ya bukaci a tantance duk wani dan kudancin kasar da ke shirin zuwa arewacin kasar.

Kudurin na kuma neman 'yan kudancin kasar su nemi izinin zama kafin su gudanar da kowace irin harka a arewacin kasar.

Kungiyar mai suna Concerned Arewa Citizens ta ce za ta gabatar da wannan kudurin doka ga majalisun dokokin jihohin arewacin kasar 19 domin zartarwa.

Tuni dai 'ya'yan wannan kungiya suka mika wa majalisar dokokin jihar Kano kudurin a ranar Alhamis.