Mosul: Mayakan ISIS sun fatattaki Kiristoci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan ISIS sun ayyana kafa daular musulunci a arewacin Iraqi

Dubban Kiristocin Iraqi daga Mosul na cigaba da kwarara yankin Kurdawa dake kusa da su suna tserewa barazana daga 'yan gwagwarmaya na Musulmi wadanda ke iko da yankin arewacin Iraqi.

A ranar Jumma'a kungiyar ISIS ta musulmin ta gitta wa Kiristocin wa'adin ranar assabar na ko dai su rumgumi addinin Islama, su kuma biya wani haraji na musamman ko kuma su fice daga birnin.

A duk tsawon rana, an rinka yin shela ta laspika a masallatai ana kira ga kiristocin da su fice daga birnin zuwa karfe sha-biyu na rana a yau asabar.

Mayakan ISIS sun ayyana kafa wata daular musulunci a yankunan arewacin Iraqin da suka kwace a cikin watan Yuni.