An kirkiro yatsu masu aiki da na'ura

Masana kimiyya
Image caption Masana kimiyya

Masana kimiyya a wata Makarantar nazarin ayyukan fasaha dake Massachusetts sun kirkiro wasu yatsu da za a rinka sarrafawa da na'ura.

Masana kimiyya a Makarantar nazarin ayyukan fasaha dake Massachusetts sun kago wata na'ura da za a rinka kara ma hannun bil'adama wadda suka ce za ta iya taimakawa wajen ayyuka na yau da kullum.

Masu bincike sun ce karin - wanda na wasu karin yatsu biyu ne - za a iya amfani da su wajen cafke wani abu, yayinda hannun kuma zai yi wani aikin na dabam.

Idan aka daura shi a wuyan hannu, zai kwaikwayi yadda wanda ya daura shi yake motsa hannun sa.

Mataki na gaba suka ce, zai zamo wani babba makamancinsa da za a kirkiro.

Karin yatsun da kungiyar wasu a Makarantar nazarin ayyukan fasaha ta Massachusetts suka kirkiro suna amfani ne da wata na'ura da aka lika a hannun dan adam don auna matsayin yatsun wanda ya daura su. Wani tsari na lissafi da aka yi ne zai rinka sarrafa na'urar zuwa yatsun da aka kirkiro, su rinka motsawa tare.

Harry Asada Farfesa a fannin nazarin ayyukan injiyan kanikanci a makarantar nazarin ayyukan fasahar ta Massachusetts ya ce,"a kulli yaumin muna amfani da wasu kayan aiki dabam-dabam, kamar wuka ko cokali mai yatsu, kuma muna tuka mota, idan kuma muka yi amfani da wadannan kayayyaki kari ne kawai ga jikin ka,"

"wannan shine kawai abinda muke so mu yi da wannan na'urar mai kwakwalwa, kana da karin wasu yatsu da karin wasu damattsa. Idan kana iya sarrafawa kuma za ka iya aiki tare da su sosai, za ka ji kari ne kawai na jikin ka."

Masana kimiyyar suka ce, na'urar za ta iya barin hannun bil-adama ya yi wani aikin na dabam, kamar motsa coffee.

Yatsun masu sarrafa kansu da na'ura, za su kasance ne a kowanne bangare na hannu - daya a wajen babban dan yatsa, dayan kuma a wajen karamin dan yatsa.

Karin bayani