Harbo jirgin Malaysia ya keta doka - Ukraine

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An yi kira da ayi bincike game da harbo jirgin fasinjan na Malaysia

Firai ministan Ukraine ya bayyana harbo jirgin Malaysia da cewa laifi ne da ya keta dokar kasa da kasa, kuma dole a hukunta wadanda suka aikata shi.

Arseni Yetsenyuk ya ce tura ta kai bango game da goyon bayan da Rasha ke bai wa masu tayar da kayar baya a gabashin Ukraine.

Kusan mutane 300 ne suka mutu a jirgin fasinjan da ya taso daga Amsterdam kan hanyarsa ta zuwa Kuala Lumpur, kuma aka harbo shi a yankin da ke karkashin 'yan tawaye.

Hukumomin Ukraine sun ce suna da shaidar cewa 'yan tawaye ne suka harbo jirgin, amma 'yan tawayen sun musanta hakan.

Karin bayani