Ana lalata sheda a wurin da Jirgin Malaysia ya fadi a Ukraine

Jirgin saman Malaysia da ya fado Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jirgin saman Malaysia da ya fado

Kwanaki biyu bayan hadarin jirgin Malaysian nan da ya fado a gabashin Ukraine, akwai kwararan alamu a wurin da hadarin ya faru dake nuna cewa ana kokarin batar da sahun al'amura.

Wakilin BBC yace ana kwashe gawarwakin mutanen da hadarin ya rutsa da su daga yankin da yan aware magoya bayan Rasha suke iko, kuma har ya zuwa yanzu ba'a yi cikakken killace wurin ba.

Shugaban Ukraine din Petro Proshenko yace kasar a shirye ta ke ta shigar da karar 'yan aware magoya bayan Rasha a gaban kotun duniya wadanda ta zarga ta harbo jirgin Malaysian a gabashin Ukraine.

Ya ce, "Ina so na tabbatar muku cewa halin da muke ciki a yanzu ya sauya kuma idan wadanda ke kiran kansu Jamhuriyar al'ummar Luhansk da Donetsk aka gano cewa kungiya ce ta yan ta'adda a cikin Ukraine to a yau za su sami tabbacin matsayin yan ta'adda a duniya baki daya."

An kwashe gawarwakin wasu mutanen da suka rasu daga wurin da jirgin saman Malaysian nan ya fado a gabashin Ukraine.

Wani wakilin BBC yace wasu ma'aikata ne wadanda suka ki baiyana kansu suka kwashe gawarwakin daga yankin da 'yan aware magoya bayan Rasha suke iko.

Tun da farko wani jagoran yan awaren a Donetsk Aleksander Borodai ya musanta zargin da gwamnatin Ukraine ta yi cewa yan aware sun badda sahun wasu alamun shaida.

Gwamnatin Ukraine dai ta ce akwai hujjoji dake nuna cewa akwai hannun Rasha wajen harbo jirgin na Malaysia.

halin da ake ciki kuma Gwamnatin Rasha ta zargi kasashen yammacin duniya da kaddamar da abinda ta kira wani yakin watsa labarai a kan Rasha.

Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce maimakon zargin yan awaren da gwamnatin Rasha ke goyon baya game da hadarin jirgin, kamata yayi gwamnatin Ukraine ta yi bayani a kan ko me na'urorin tsaron sararin samaniyarta ke yi a yankin.

Kusan dai mutane 300 ne suka mutu a lokacin da ga alama aka harbo jirgin fasinjar na kamfanin zurga zurgar jiragen sama na Malaysia yayi da yake kan hanyarsa ta zuwa Kuala Lumpur daga Amsterdam.