Yaki da satar fasaha a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption Gwamnati ta ce shiri ne na fadakar da mutane kamar iyaye wadanda ba su sani ba, game da yadda ake amfani da intanet dinsu.

Daga yanzu mutanen da suke satar juyar kida ko fim akai-akai za su rika samun wasikar gargadi ta intanet cewa abin da suke yi ya saba ka'ida.

Gargadin wani bangare ne na wani gagarumin shirin wayar wa da mutane kai a kan hakkin mallakar fasaha da kuma hanyoyin shari'a na amfana fasaha.

A shirin wanda za a fara daga shekara mai zuwa, za a rika aika wa wanda ake zargin satar fasahar gargadi har sau hudu a shekara.

Amma kuma idan mutane suka yi watsi da gargadin babu wani mataki da za a dauka a kansu.

An bullo da tsarin ne sakamakon dambarwar shekara hudu tsakanin kamfanonin samar da intanet da na kade-kade da fina-finai.

Hakkin mallakar hoto PA

Gwamnatin Birtaniya ta kuma yi alkwarin bayar da gumamwara fam miliyan 3 da rabi domin wayar wa jama'a kai don amfani da hanyoyin da suka dace na sauraren kade-kde da kallon fina-finai.

Birtaniyan za ta yi hakan ne domin tallafa wa harkar kirkire-kirkire.

Gwamnati ta yi kiyasin fannin na kirkire-kirkire yana samar da fam biliyan 71 ga tattalin arzikin Birtaniya.

Yana kuma samar da ayyuka miliyan 1 da dubu 68 a kasar.