Fulani sun koka da yawan sace musu shanu

Hoton wani Bafulani makiyayi
Image caption Hoton wani Bafulani makiyayi

A Najeriya yayin da ake cigaba da fuskantar kalubalen tsaro wasu rugage na Fulani a kewayen birnin Abuja su ma sun koka bisa yadda wasu 'yan bindiga suke yawan kai musu hari da kuma yin awon gaba da shanunsu.

Fulanin sun ce a wasu lokutan ma akan sami hasarar rayuka a irin wannan farmaki da ake yawan kai musu cikin dare.

Sun kuma koka da rashin jami'an tsaro duk da yake suma 'yan kasa ne kuma suna bukatar kariya.

Wannan batu dai na sacewa ko kuma awon gaba da shanun Fulani na nema ya zama ruwan dare a kauyukan arewacin Najeriya da dama.

Karin bayani