Boko Haram: Kwamitin Dangote na rangadi

Alhaji Aliko Dangote Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kwamitin zai kafa sansani domin wadanda ambaliya ke rabawa da gidajensu a kowace jiha.

Wani kwamiti da gwamnatin Najeriya ta kafa domin taimakawa wadanda bala'o'i suka fada wa a sassan kasar daban-daban na ci gaba da rangadin jihohin da rikice-rikicen suka shafa.

A bara ne dai aka nada kwamitin karkashin jagorancin hamshakin attajirinan na Afirika, Alhaji Aliko Dangote, domin taimaka wa wadanda bala'o'I suka shafa da kayayyakin masarufi.

Asali dai an kafa kwamitin ne domin taimaka wa wadanda ambaliyar ruwa ta raba da matsugunansu, amma ganin yadda hare-haren kungiyar Boko Haram da fadace-fadacen kabilanci ke ci gaba da rutsawa da daruruwan jama'a, kwamitin ya fadada ayyukkansa domin taimaka musu; inji Dr Sani Abubakar Lugga,Wazirin Katsina, daya daga cikin jami'an kwamitin.

''Mun zabi jihohi goma kamar su Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Bauchi har da su Katsina, inda dai aka samu rikici; ko na Boko Haram ko na Fulani da manoma din nan,'' inji shi.

Karin bayani