Tarayyar Turai ta soki Kamfanin Apple

Image caption Wasu iyaye sun kadu da ganin yadda ake cazar kudi kan manhajar da ake saukowa da ita kyauta.

Hukumar Tarayyar Turai ta soki kamfanin Apple kan rashin fito da wasu kwararan tsare-tsare da gaggawa domin hana rudin abokan huldarsa da ba su damar sauko da manhaja kyauta.

Manhajoji da yawa da mutane ke so ana sauko da su ne kyauta, amma an tsara su ne ta yadda za su ja hankalin masu amfani da su don su biya kudi domin habbaka musu manhajojin wasannin da da ma suke da su.

A yanzu hukumar na kokarin tilastawa kamfunan Apple da Google wadanda suka fi kowa tallata manhajoji da su bayyana komai karara.

Amma dai ta ambaci kamfanin Apple ne kawai kan rashin nuna shirin yin gyara.

''Abin takaici har yanzu babu wasu kwararan matakai na gaggawa da Apple ya dauka don magance matsalar da ta shafi biyan kudi'' inji hukumar a cikin wata sanarwa.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfunnan Apple ga Google da kuma Amazon duk sun fuskanci matakin shara'a na karar da ta shafi neman hakkin rudin abokin hulda a Amurka.

Hukumar ta ce hukumomin kasashe na da zabin daukar matakin shara'a kan kamfunnan da ba su bi sabbin ka'idojin Tarayyar Turai na sauko da manhaja kyauta ba.

Acikin wata sanarwa, kamfanin na Apple ya ce yana daukar matakai fiye da kowanne domin kare iyaye masu hulda da shi.

''Wadannan matakan sun zarce na wasu da ke cikin wannan sana'ar nesa,'' inji mai magana da yawun kamfanin Apple.

''A kodayaushe muna aiki domin kara karfafa matakan kare abokan huldarmu da tun can muke da su, kuma muna kara wasu sabbin matakan da manhajarmu ta iOS 8, da za ta ba iyaye karin ikon kayyade irin manhajojin da yaransu za su iya saye a shagon Apple'' inji shi.

An ce shi ma Google ya yanke shawarar fito da sauye-sauye da dama wadanda za su fara aiki daga watan Satumba.

Karin bayani