Gaza: Karancin kayan agaji

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Isreala na ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta kasa a zirin Gaza

Majalisar dinkin duniya ta ce, kayayyakin agajin taimaka wa Palasdinawa 50, 000 da suka fake a makarantunta da ke Gaza, suna kan karewa.

Wani jami'i da ke kula da ayyukan jinkan, Robert Turner, ya ce, yawan mutanen da ke tserewa rikicin, ya wuce yadda aka yi tsammani.

Ya ce yanzu, sabbin zuwa sai dai su rika kwanciya a kan dabe kawai.

Kawo yanzu dai an bayar da rahoton mutuwar Palasdinawa kusan 350, tun lokacin da Isreala ta fara kai hare hare kan Gaza a kwanakin nan.