A daina Sa ido kan harkokin mutane

Navi Pillay Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Navi Pillay

Huhukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin duniya ta yi gargadin cewa, gwamnatoci da dama na cigaba da amincewa da shirin sa ido da binciken abinda dimbin mutane ke yi.

Hukumar ta kara da cewa tatattara bayanai da ake yi na dimbin mutane don karfafa binciken sirrin su, bai wajaba ba ko kuma bai dace ba.

Rahoton ya zo ne a daidai lokacinda Brittaniya ta amince da wata dokar gaggawa da ta umurci kamfanonin wayoyin salula da kamfanonin dake samar da hanyoyin sadarwa na Internet ko "yanar-gizo" su rinka tattara bayanai na mutanen da suke mu'amalla da su.

Ofishin Navi Pillay, Kwamishiniyar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin duniya ya rubuta takardar, wanda yace, wannan ya nuna abin damuwa na karancin fahimtar dalilan da suka sanya gwamnatoci suka amince ko kuma fara sa ido a kan abinda mutane ke yi ta hanyoyin sa da zumunta na zamani.

Mr Pillay tace, sa ido kan abinda dimbin mutane ke yi, yana zama wata halayya mai hadari a maimakon wani mataki na dabam ga gwamnatoci.

Wadannan shire-shire ala tilas suna shiga harkokin sirri na mutane, don haka dole ne gwamnatoci su kara tashi tsaye don tabbatar da cewa, wannan kare 'yanci na mutane ba wai wani abu ba ne da ko dai aka nuna son zuciya ko kuma ya saba ma doka.

Ms Pillay tace idan gwamnatoci suka maida kai wajen neman bayanai game da 'yan kasarsu, to kamata ya yi su maida kai su tabbatar da dalilan da suka sanya su yin haka, su kuma sa ido don kada a wuce gona da iri wajen amfani da wadannan bayanai.

Rahoton yace, dole a baiwa jama'a damar sanin dokokin da suka zayyana yadda za a rinka sa ido kan harkokinsu tare da bayanin ainihin dalilan da suka sanya ake sa ido a kan harkokin na su.

Har ila yau kuma rahoton ya ce, dalilan ba su ta-ka kara suka karya ba, na matakan da aka dauka na tilasta ma kamfanonin sadarwa da na wayoyin salula da sauransu na rike bayanai a kan abinda mutane suka yi ta hanyar sada zumunta ta zamani da kuma wanda suka yi magana da shi.

Karin bayani