'Yan Boko Haram sun sace matar wani kusa a Kamaru

'Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram

Hukumomi a Kamaru sunce 'yan kungiyar Boko Haram ta Najeriya,sun kai wasu tagwayen hare hare a can arewacin kasar, inda suka sace duka matar wani babban dan siyasa da kuma wani shugaban addini a yankin.

An dauki matar mataimakin Pirayim Minista Amadou Ali da yar aikin gidanta daga garin Kolofata kusa da kan iyaka da Najeriya.

Haka kuma an sace wani shugaban addini na yankin Seini Boukar Lamine da iyalansa daga gidansu a garin na Kolofata dai.

Mutane da yawa ne aka kashe hade da dan uwan mataimakin Pirayim Ministan.

An bayar da rahoton dai fada na ci gaba tsakanin Boko Haram da soji.

A ranar juma'a 'yan kungiyar fiye da 20 ne aka daure a Kamaru bayan da aka same su da laifi na kitsa tayar bore.