Nigeria za ta dauki mataki a kan Damboa

'Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mazaunin garin ya ce duk wadanda ke cikin garin yanzu 'yan Boko Haram ne.

Gwamnatin Nigeria ta mayar da martani ga rahotannin da ke cewa 'yan Boko Haram sun kwace garin Damboa na jihar Borno tare da kafa tutarsu a can.

Gwamnatin ta ce in gaskiya ne hakan ta faru, dakarun kasar za su dauki matakin da ya dace.

''Babu wani mahalukin da ya isa ya yanka wani sashen Najeriya ya ce ya zama nasa; ina son in tabbatar muku duk wanda ya yi wannan kuskuren akwai maganinsa.'' Inji Mr. Mike Omeri, shugaban cibiyar samar da bayanai kan yaki da ta'addanci a kasar.

Hakan dai ya biyo bayan wani hari ne da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai a garin inda suka kashe mutane da yawa tare da kona wasu sassan garin ranar Alhamis.

Karin bayani