Dokar yaki da masu satar fasahar mutane

Mutane Birtaniya dake satar fasahar mawaka da kuma ma su shirya fina-finai nan bada jimawa zasu soma samun sakonin e-mail na gargadi da za su sanar su aikin da suke yi haramtacce ne.

Gargadin na cikin shirin da aka bulo da shi domin fadakar da mutane akan yadda ake amfani da fasahar mutane kamar yadda doka ta tanada.

Daga badi , za'a rika turawa mutane da ake zargi da satar fasahar wasu da sakoni gargadi har sau 4 a kowace shekara.

Sai dai ba bu wani mataki da za'a dauka, ko da mutane sun yi watsi da gargadin da aka yi masu.

Tsarin ya biyo bayan shekaru hudu da aka yi kai ruwa rana tsakanin kamfanonin samar da internet watau ISPs da kuma kamfanonin dake wakiltar mawaka da kuma masu shirya fina-finai.

Dokar da aka zartar a shekarar 2010 da ake kira Digital Economy Act ta fayyace irin matakan da ya kamata a dauka akan masu laifi kuma ta nemi a dakatar da internet din masu satar fasahar mutane idan sun yi watsi da jerin gargadin da aka yi masu.

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

"Abu ne me wahala"

Masu fasaha sun nemi sakonin e mail din a kan su fayyace irin hukuncin da za'a dauka akan masu satar fasahar wasu .

Shekarun da aka shafe a tattaunawar da gwamnatin Birtaniya ta jagoranta ya sa an kirkiro da wani shiri na aikewa da sakonin e mail na gargadi.

Manyan kamfanonin internet na Birtaniya irinsu BT, da Talk Talk da Virgin da kuma Sky sun sa hanu akan tsarin kuma ana sa ran nan gaba kananan kamfanoni zasu sa hanu akan tsarin.

Hakkin mallakar hoto bbc

"Sauya ra'ayin mutane"

Gwamnati ta yi kiyasin cewa bangaren masu fasaha na kasar na samar da fam biliyan 71 ga tattalin arzikin kasar tare kuma da samar da ayuikan yi fiye da miliyan daya.

Shugaban kamfanin BPI , Geoff Taylor,ya ce sai da aka shafe tsawon lokaci kafin aka cimma matsaya akan yarjejeniyar Vcap.

Ya ce duk da cewa dokar ba za ta iya hukunta wani ba amma za ta taimaka wajen sauya ra'ayin mutane.