An saki Ezekwesili bayan tsare ta a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Najeriya ta dauko hayar wani Ba Amurka jami'in hulda da jama'a domin mai da martani ga fafutukar kungiyar

Jami'an tsaro a Nigeria sun tsare daya daga cikin shugabannin kungiyar fafutukar ceto 'yan matan Chibok, Obiageli Ezekwesili kafin daga bisani a sake ta.

An karbe takardun tafiye-tafiye na tsohuwar ministar ilimin a lokacin da take kokarin shiga jirgi zuwa London a filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ezekwesili ta bayyana a shafinta na Twitter cewa tana kan hanyarta na zuwa London ne domin shiga wani shiri na turanci na BBC mai suna HardTalk, amma jami'an SSS sun kwace mata Fasfo.

Batun da ya kai ga matsin lamba ga gwamnati bayan ya ja hankalin jama'a a dandalin na sada zumunta, abin da ya sa kuma aka mayar mata da fasfonta.

Kungiyar ta #BringBackOurGirls mai fafutukar ceto 'yan matan Chibok ta zame wa gwamnati karfen kafa tun bayan kafuwarta, watanni uku da suka wuce.