Tsohon Minista Rilwanu Lukman ya rasu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Margayi Dr Rilwanu Lukman

Tsohon ministan albarkatun man fetur a Nigeria, Dr Rilwanu Lukman ya rasu a kasar Austria.

Dan shekaru 76, Lukman wanda Injiniya ne ya rike mukamin ministan a gwamnatoci da dama a Nigeria sannan kuma ya shafe shekaru shida a matsayin Sakatare Janar na kungiyar kasashen masu arzikin man fetur watau OPEC.

Sannan kuma sau uku yana rike mukamin shugaban kungiyar ta OPEC watau a shekarar 1986 da 1989 da kuma 2002.

Kungiyar OPEC a wata sanarwa ta nuna alhininta game da rasuwar Dr Rilwanu Lukman, inda ta bayyana shi a matsayin gwarzo wanda ya yi aiki tukuru tare da sadaukar da kai.

An haife shi ne a birnin Zaria da ke jihar Kaduna a ranar 26 ga watan Agustan 1938, sannan kuma ya yi karatu a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria da kuma Imperial College a London.