Jonathan ya gana da Sarki Sanusi na Kano

Sanusi Lamido da Jonathan Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Jonathan na yi wa Sarki maraba da zuwa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da sabon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu inda suka yi bude baki tare a ranar Laraba.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin shugabannin biyu tun lokacin da Sarki Sanusi yake rike da mukamin gwamnan babban bankin Najeriya CBN.

A lokacin Mallam Sanusi ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Jonathan da kin shigar da wasu kudaden man fetur cikin asusun gwamnatin tarayya, abin da ya sa aka yi zargin gwamnatin Jonathan ta yi sama da fadi da su.

Daga nan ne kuma aka dakatar da Mallam Sanusi daga mukaminsa bisa zargin aikata ba daidai ba, abinda ya sa wasu ke zargin bi-ta-da-kulli gwamnatin tarayya ta yi masa saboda zargin da ya yi mata.

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Sarki Sanusi na II da Shugaba Goodluck Jonathan

Wannan rashin jituwar ta ci gaba har zuwa lokacin da aka nada Mallam Sanusi Lamido a matsayin Sarkin Kano, kuma har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bai fitar da sanarwar taya shi murna ba kamar yadda aka saba.

Da alama ganawar ta jiya ita ce ta farko tsakanin mutanen biyu tun lokacin da aka yi dambarwar nada Sarki Sanusi na biyu.

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Sarakunan gargajiya a fadar shugaban kasa

Shugabannin biyu sun gana ne a lokacin bude baki da shugaba Jonathan ya yi da sarakunan gargajiya Musulmi.

Karin bayani