Madaurin kujera ya yi sanadin kashe yaro

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Afrika ta Kudu na cikinkasashen da suka fi kowa masu aikata lafuka kuma kwace mota ya zama ruwan dare

Wani yaro dan Afrika ta Kudu dan shekara hudu ya rasa ransa a wani yunkuri na sace motar da ya ke ciki a Johannesburg.

Taegrin Morris na tare da mahaifiyarsa da kuma wata 'yar uwarta a cikin motar a lokacin da lamarin ya auku a ranar Asabar da daddare.

Sai kawai mutane uku dauke da makamai suka auka musu inda suka yi kokarin kwace motar, sai dai kafar yaron ta makale a madaurin kujerar motar duk da yunkurin da uwar yaron da kuma 'yar uwarta suka yi na fito da shi daga motar.

Barayin sun tuka motar a guje suna jan yaron a kan titi, kuma an gano motar kilomita hudu daga inda lamarin ya auku da gawar yaron a kusa da ita.