Gargadi ga masu amfani da intanet

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shafin Facebook ya rika fitar da wadannan hanyoyi na zamba da aka ankarar da shi

Labarin faduwar jirgin saman Malaysia, wanda ya hallaka mutane 298 a Ukraine ya zama hanyar da masu zamba ta intanet ke yada shafuka na batsa.

Masana harkokin tsaro na gargadin masu mu'amulla da intanet akan su lura su kiyaye.

A daya daga cikin irin wadannan ne aka boye wani shafin hotunan batsa, a matsayin hanyar samun bidiyon hadarin jirgin saman.

Image caption Wani tarkace daga cikin kayan fasinjojin jirgin

An sanya shafin a Facebook da sunan wanda aka sadaukar domin daya daga cikin wadanda suka rasu a hadarin.

Shafukan Twitter da dama da ke nuna suna dauke da labarin ne, suna dauke da hanyoyin shafukan zamba.

Wani daga cikin kwararru akan tsaron intanet ya ce kamfanonin sada zumunta na intanet ne alhaki ya rataya a wuyansu su fitar da su.

Wani daga cikin kwararrun, Ricahrd Cox, ya ce, abu ne da ya zama ruwan dare mazambata su yi amfani da wani lamari da ake yawan tattaunawa a kansa wajen aikata zamba.

Akan wannan salo masu shafukan sun bukaci duk wanda ya ga alamar wannan hanya ta zamba da ya sanar da su, domin daukar mataki.