Mayaka sun mika na'urar nadar bayanai

Jirgin Saman Malaysia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tarkacen jirgin saman Malaysia da ya fadi

Wani shugaban mayakan 'yan a ware a gabashin Ukraine ya mika naurarorin nadar bayanai na jirgin saman Malaysia , da ya fadi ranar alhamis din da ta gabata zuwa ga kwararu a garin Donetsk

A jiya ne dai kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudiri ba tare da hamayya ba.

Kudirin ya yi kira da a bada kariya, da kuma cikakkiyar dama ga masu bincike na kasashen duniya su samu kaiwa ga inda aka harbo jirgin saman Malaysia a gabashin Ukraine.

Daftarin kudirin, wanda Australiya ta gabatar ya bukaci dukkan kungiyoyi masu daukar makamai da su daina daukar duk wani mataki da zai kawo cikas ga aikin bincike a inda hadarin ya auku.

Kudirin ya kuma bukaci a mutunta gawarwakin wadanda suka rasun, ta yadda za a mika gawarwakin ga iyalansu su cikin mutunci.

Karin bayani