Burtaniya na sayar wa Rasha kayan soji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Burtania na gaba-gaba wajen adawa da Rasha a kan Ukraine

Wani rahoto da 'yan majaisar dokokin Burtaniya suka fitar ya nuna cewa har yanzu gwamnatin kasar na bari ana sayar wa Rasha kayan soji duk da alkawarin da ta yi na dakatar da hakan kan rikicin Ukraine.

An buga rahoton ne jim kadan bayan Firaminista David Cameron ya bukaci kungiyar kasashen Turai ta sanya wa Rashan, takunkumin makamai, ya kuma soki Faransa kan yadda ta ci gaba da sayar wa sojin ruwa na Rasha wasu jiragen ruwa na yaki biyu.

A martanin da suka mayar shugabannin Faransa sun gaya wa Birtaniya cewa, kamata yayi ta fara kawo karshen rawar da ta ce wasu 'yan kalilan din masu fadi a ji na Rasha ke takawa a harkokin kudi na London.