Rikicin Iraki na ruruta fada tsakanin bangarori a internet

Wani bincike da kamfanonin tsaro suka yi ya nuna cewa baya ga rikicin da ake fuskanta a kasar Iraki akwai kuma fadan da bangarori ke yi a shafukan internet.

Wasu bangarori kan yi amfani da shafukan sada zumunta wajen neman magoya baya tare kuma da yada farfaganda yayinda wasu bangarorin na daukar masu satar bayanai aiki domin samar masu da bayanan siri.

Masu zamba ta internet na amfani da rikicin wajen yaudarar mutane su fada tarkonsu .

Rikicin cikin gida

Shugaban kamfanin Intel crawler Andrew Komarov ya ce bangarorin da wanan lamari ya shafa sun hada da kungiyoyin cikin gida dake amfani da manhajar Malware wajen tattara bayanan siri .

Ana amfani da wata manhaja da ake kira Njirat kuma ta taikmawa wasu kungiyoyi kirkiro shafukan internet da suke da iko akansu.

Ta wannan hanyar ce kungiyoyin ke satar bayanai ko amfani da kamarar Kyumfuta ko makarufo domin sa ido akan ayuikan wasu.

A garuruwa hudu da suka hada da Bagadaza, Basra da Mosul da kuma Erbil ake fuskantar wanan matsala.

Shugaban kamfanin Intel Crawler Andrew Komarov ya ce ana tattara bayanan siri akan masu zanga-zanga , jam'iyyun adawa da kuma fararen hula ko gwamnati da kuma sauransu.

Hakkin mallakar hoto AFP

Shi ma kamfanin tsaro na Kaspersky Labs ya ce tashe tashen hankulan da ke fuskanta a Iraki da Syria da kuma sauran kasashen larabawa ya sa ana samun jerin batutuwa akan fadan cacar baka da bangarori ke yi da juna a shafukan internet.

Me Bincike Mohamad Amin Hasbini ya ce rikicin da ake cigaba da fuskanta na daga cikin abubuwan dake ruruta fadan cacar baka sai dai ba bu cikakken bayani akan ko akwai manufar siyasa a ciki lamarin.

Ya ce an yi amfani da batutuwa da suka shafi 'yan shia, da alakar da ke tsakanin Shugaba Assad na Syria da kungiyar ISIS, da kuma bayanai akan wuraren da ke fama da tashe tashen hankula a cikin manhajar Malware.

Hasbini ya ce manhajar Malware da aka yi amfani da ita wajen kai hare hare ana kuma yadda ta a kafafofin sada zumunta irinsu Facebook da You Tube da Skype da kuma Whatsapp.