Nigeria ta haramta yi wa 'yan ci-rani rijista

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan arewacin Nigeria na zargin ana gallaza musu a Kudu

Gwamnatin Nigeria ta haramta tisa keyar mutane daga wasu jihohin kasar zuwa jihohinsu na asali kamar yadda yake faruwa yanzu haka a kudancin kasar.

Haka nan kuma an haramta wa wasu jihohin kasar yi wa 'yan ci-rani daga wasu sassan kasar rajista kafin su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Majalisar tsaron Nigeria karkashin jagorancin Shugaba Goodluck Jonathan ce ta yanke wannan shawarar zaman da ta yi a Abuja.

Umurnin majalisar ya biyo bayan yadda wasu jihohin kudu maso gabashin Nigeria ke yi wa 'yan arewacin kasar rijasta ko kuma tisa keyarsu zuwa jihohinsu na asali.

A cikin watan Yuni ne aka tsare wasu 'yan arewacin kasar kusan 500 a jihar Abia bisa dalilan tsaro, lamarin da ya janyo cece-kuce a Nigeria.

Karin bayani