Shekaru 20 na mulkin Jammeh a Gambia

Image caption Jammeh ya cire Gambia daga cikin kungiyar Commonwealth

A ranar Talata ne shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya cika shekaru 20 cif a kan karagar mulki, bayan wani juyin mulkin soji.

Sai dai daga bisani kisan da aka yi wa mutane a kasar ciki har da kisan gilla ya bata juyin mulkin da ya yi wanda ba a zubar da jini ba.

Lokacin Jammeh yana karamin hafsan soji mai shekaru 29 ya bayyana dalilansa na yin juyin mulki da cewa shugaban kasar na farko bayan samun 'yancin kasar Sir Dawda Jawara ya dade a kan mulki.

Sai dai shekaru 20 bayan nan, shugaban mai shekaru 49 ya shaida wa BBC lokacin da aka sake zabensa a shekarar 2011 cewa zai mulki Gambia "Har karshen rayuwarsa" idan har mutane sun zabe shi.

Ya ce ya cimma nasarorin da Burtaniya wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka ba ta cimma ba a 'yar karamar kasar da ke Afrika ta yamma.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban ya sa an daina amfani da harshen Ingilishi a kasar

A cikin shekaru 20, gwamnatin Yahya Jammeh ta sauya kasar sosai ta fuskar samar da ababen more rayuwa, kamar gina tituna a fadin kasar da asibitoci da makarantu da jami'a da filin jiragen sama, kuma ya yi alkawarin samar da wutar lantarki a wasu daga cikin mayna biranen kasar.

Sai dai ya gamu da suka sosai game da dadewa da ya yi a kan mulki da ayyukan keta hakkin bil'adaman da ya aikata da kuma daukar matakan da yake na bazata.