Gaza: Mutanen da aka kashe sun haura 600

Hakkin mallakar hoto AP

Isra'ila tana ci gaba da kai farmaki akan wasu wurare a yankin Gaza, yayin da yawan Palasdinawan da suka kashe ya haura dari shida.

Cikin daren jiya da ya gabata dakarun Isra'ila sun kai hari akan wurare saba'in da suka hada masallatai da filayen wasanni a yankin Gaza.

Pira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ya kamata kasashen duniya su dorawa Hamas laifi kan yawan yin watsi da tayin tsagaita wuta.aza

Wannan na faruwa ne yayin da kuma sakataren hulda da kasashen wajen Amurka, John Kerry yake kara kaimi ta fuskar diplomasiyya domin ganin an tsagaita wuta.