Jonathan ya gana da iyayen 'yan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jonathan ya dauki alkawarin ceto 'yan matan da aka sace

Bayan kusan kwanaki 100 da sace 'yan mata dalibai a Chibok, shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya gana da iyayen 'yan matan da aka sace.

Dalibai 51 da suka kubuce daga hannun 'yan Boko Haram da kuma iyayen yara fiye da 100 ne suka halarci ganawar a fadar Shugaban Nigeria da ke Abuja.

A makon da ya gabata ne iyayen yaran suka kauracewa ganawa da Mr Jonathan bisa wasu batutuwa na rashin fahimtar juna.

Mr Jonathan na shan suka saboda rashin ganawa da iyayen yaran tun farko da kuma batun rashin hobbasa a kokarin ceto 'yan matan da aka sace tun a watan Afrilu.

Kungiyar Boko Haram wadda ta sace 'yan matan fiye da 200 ta ce za ta iya musayarsu da mayakanta da ake tsare da su a gidajen yarin Nigeria.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane dubbai da muhallansu a yayinda wasu rahotannin suka ce kungiyar ta kafa tutocinta a wasu sassan jihar Borno.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yar Pakistan Malala Yousafzai ta tattauna da wasu 'yan Chibok

'Gudun Hijira'

Rahotanni na cewa fiye da mutane dubu 15 ne suka tsere daga garin Damboa da kewayansa, a jihar Borno da ke Nigeria, sakamakon munanan hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.

Mutanen sun samu mafaka a garin Biu a cewar shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar, NEMA.

Hukumomi a yankin sun ce, kawo yanzu an tabbatar da mutuwar sama da mutane 40 a harin da 'yan kungiyar suka kai garin na Damboa ranar Juma'a.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyayen 'yan matan na cikin matukar damuwa
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu daga cikin iyayen sun gamu da ciwon hawan jini

Karin bayani