Bam ya hallaka mutane 25 a Kaduna

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan ne karo na biyu da Bam ya tashi a Kaduna cikin wata guda

Rahotanni daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria na cewar wata mota makare da bam ta fashe inda ta hallaka mutane akalla 25 tare da raunata wasu da dama.

Rundunar 'yan sandan jihar sun tabbatar da afkuwar lamarin tare da rasuwar mutane 25.

Wani shaida ya bayyanawa BBC cewar lamarin ya faru ne a kan titin Isa Kaita gab da titin Ahman Pategi da ke Unguwar Sarki a Kaduna.

A cewarsa, bam din ya fashe ne jim kadan bayan da wani babban malamin addinnin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya wuce da ayarin motoci bayan kamalla tafsirin Alkur'ani a dandalin Murtala da ke tsakiyar Kaduna.

Sai dai babu abinda ya samu Sheikh Dahiru Usman Bauchi da 'ya'yansa.

Mutumin da ya shaida lamarin ya kara da cewar baya da gawarwakin da ya kirga akwai mutane da dama da suka samu raunuka sannan kuma mutane na cikin firgici.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin, amma kuma kungiyar Boko Haram ce ke kaddamar da hare-hare a Nigeria inda ta hallaka dubban mutane tun daga shekara ta 2011.