Sojojin Nigeria na gudu daga aikin soji

Image caption Dakarun Nigeria na jiran shiga fagen fama

Babban hafsan dakarun sojin kasa a Nigeria Laftanar Janar Keneth Minimah ya bayyana cewar wasu sojoji na gudu daga aiki saboda tsoron Boko Haram.

A cewar Minimah lamarin abin Allawadai ne kuma ya nuna cewar mutanen ba su dace da shiga aikin soja ba.

Ya kara da cewar sojan asali ba zai guje wa yaki ba, saboda an dauke shi aiki ne domin ya kare martabar kasarsa kuma ya je fagen daga.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin hukumomin Nigeria ba sa lura da sojojin da ke yaki da Boko Haram hakkokinsu yadda ya kamata.

Bayanai sun nuna cewar dakarun Nigeria da ke yaki a Borno da 'yan Boko Haram ba su da cikakkun kayan aiki abin da ya sa ake fuskantar hasarar rayuka a bangaren sojojin.

A 'yan watanni da suka wuce, wasu sojoji sun yi bore a Maiduguri inda suka harbi motar kwamandansu bisa zargin cewar ya yi kuskuren tura abokan aikinsu wadanda 'yan Boko Haram suka yi wa kwantan bauna.