An gano tarkacen jirgin Algeria a Mali

Air Algeria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Air Algeria

An gano tarkacen jirgin saman nan na kasar Algeriya wanda ya bace lokacinda ake ruwan sama da tsawa da sanyin safiyar Alhamis a kasar Mali.

Gwamnatin Faransa ta ce, ta tura sojoji su killace wurin da jirgin saman ya fadi tare da tattara shaida.

'Yan kasar Faransar ne kusan rabi na fasinjan jirgin saman 116.

Jirgin ya taso daga Burkina Faso zuwa Algeria.

Hukumomin Burkina Faso sun ce babu wanda ya tsira a jirgin saman, yayinda kuma suka yi shelar zaman makoki na kwanaki biyu a kasar.

Karin bayani