Jirgin Air Algerie ya bata a sama

Hakkin mallakar hoto Arsiv
Image caption Mutane 116 ne a cikin jirgin saman

Kamfanin jiragen saman Algeria, Air Algerie ya ce gaza sadarwa da daya daga cikin jiragensa da ya taso daga Burkina Faso zuwa birnin Algiers a yankin Sahara.

Kamfanin ya ce sadarwa ta katse da jirgin kimanin minti 50 da tashinsa daga birnin Ouagadougou a Burkina Faso.

An yi wa jirgin ganin karshe ne da karfe 1:55 agogon GMT, inda ake sa ran saukarsa birnin Algiers da karfe 5:10 na safe.

Kamfanin Spanish airline-Swiftair da ya mallaki jirgin amma kamfanin Air Algerie ke sufuri da shi, ya ce jirgin Fasinjan kirar AH 5017 na dauke da mutane 110 tare da ma'aikata shida.

Jami'an Air Algerie sun ce kamar yadda tsare-tsaren sufurin jiragen sama suka tanada, kamfanin ya kaddamar da shirin ko-ta-baci