Dakaru 2,800 domin yaki da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An zargin Boko Haram ta kafa tutocinta a Damboa

Nigeria da wasu kasashe uku sun sha alwashin kafa runduna ta musamman mai dakaru 2,800 don tunkarar kungiyar Boko Haram.

Ministocin tsaron Nigeria, Kamaru, Chadi da kuma Niger sun ce kowacce kasa za ta bada gudunmowar dakaru 700 a cikin rundunar.

Ministan tsaron Niger, Karidio Mahamadou ya ce sun lashi takobin kawar da kungiyar.

A wasu lokutta, kungiyar Boko Haram tana kai hare-hare a kan kasashen da ke makwabtaka da Nigeria.

Ana zargin kungiyar da tarwatsa gadar Ngala mai matukar muhimmanci ta fuskar sufurin kayayyaki tsakanin jihar Borno ta Nigeria da kuma Jamhuriyar Kamaru.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jihohi uku a Nigeria na karkashin dokar ta-baci

Ministocin tsaron kasashen hudu wadanda suka gana a Yamai a ranar Laraba, sun ce za su ci gaba da tattaunawa kan barazanar da Boko Haram ke yi wa kasashen.

A cikin watan Mayu ne, kasashen hudu wadanda mahadarsu take a tafkin Chadi, suka ce za su dinga musayar bayanan sirri don tabbatar da tsaro.