An yi tabarau na taimakon masu ciwon suga

Tabarau na masu ciwon suga Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tabarau na masu ciwon suga

Katon kamfanin nan na harhada magunguna Novartis ya amince a wata yarjejeniya da suka kulla da kamfanin sadarwa ta internet Google su samar da wani ruwan tabarau mai kwakwalwa da zai taimaka wa masu ciwon suga auna matakin suga na jikinsu.

A watan Janairu ne aka fara nuna samfur na ruwan tabaran na Google.

An shirya shi ne yadda zai auna matakin suga na jikin wanda ya sanya shi, sannan kuma ya kai bayanan ga wata wayar salula ko Computa.

Fasahar sanyawa ko daura wani abu ita ce yanzu ake kallo a matsayin wani fanni na cigaba, yayinda kamfanoni da dama ke hankokron samad da kayayyaki irin wadannan na kiwon lafiya.

Ruwan tabaran yana amfani ne da wata 'yar karamar matattarar bayanai wadda aka hada da wata 'yar na'ura masu sunsunar suga na jikin dan adam.

Kamfanin sadarwa na Google ya ce 'yar karamar na'urar mai tattara bayanai da na'urar mai sunsuno sugan, saboda kankantarsu, sun yi kama da wasu 'yan kananan kyalkyali da kuma wata eriya wadda kaurin ta bai wuce gashi daya na kan mutum ba. Tace, samfurin ruwan tabaran zai rinka samun bayanai cikin dakika daya.

Kamfanin harhada magungunan na Novartis ya fada cikin wata sanarwa cewar wannan fasaha tana iya zamowa wata hanya ta kula da lafiyar ido.

Joe Jimenez babban jami'i na kamfanin yace, wannan muhimmin mataki zai iya zama wata hanya ta zarce hanyoyin al'ada da aka sani na maganin cututtuka, tun daga wannan na'ura ta kula da lafiyar ido.

Sergey Brin daya daga cikin mutanen da suka kirkiro kamfanin Google ya ce, "mafarkin da muke da shi, shine na amfani da fasaha ta baya-bayan nan wajen yin kananan naurori da za su taimaka wajen inganta lafiyar miliyoyin mutane.

Za a dai dauki lokaci kafin a yi na'ura irin wannan don sayar ma jama'a.

Karin bayani