An yi wa maza yankan rago a Gamboru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekau da mukarrabansa

Rahotanni daga garin Gamborou Ngala na jihar Borno sun nuna cewar 'yan kungiyar Boko Haram sun afkawa garin, tare da yi wa wasu magidanta yankan rago.

Hakazalika an kashe wasu mutanen da dama a kan hanyar Maiduguri zuwa Gamborou.

Bayanai daga garin Gamborou Ngala na cewa mutane da dama na ta ficewa suna tsallakawa makwabciyar kasar Kamaru domin neman mafaka sakamakon tashin hankalin.

Baya ga kuncin rayuwa da suke fuskanta, mutanen da suka rage a yankin sun ce suna cikin zaman zullumin abin da ka iya faruwa a gare su.

A ranar Talata ne 'yan Boko Haram suka tarwatsa wata babbar gada da ke Ngala abinda ya haddasa katse daya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri tsakanin Najeriyar da kasar Kamaru.

Hakan na zuwa ne a yayinda babban hafsan sojin kasar Najeriya, Laftanar Janar Kenneth Minimah ke cewa wasu sojoji sun arce daga bakin aikinsu saboda tsoron Boko Haram.