Bore kan matsin tattalin arziki a Ghana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Mahama na fuskantar matsin lamba

Al'ummar Ghana fiye da dubu biyu ne ke gudanar da zanga-zanga a Accra kan abun da suka kira wasarairan da gwamnati ke yi wa tattalin arzikin kasar.

Babbar kungiyar kwadagon Ghana ce ta shirya wannan zanga-zanga a fadin kasar, a karon farko tun bayan hawan Shugaba John Dramani Mahama kujerar mulki a watan Janairun bara.

Shugaba Mahama na fuskantar matsin lamba kan ya farfado da tattalin arzikin wannan kasa mai albarkar man fetur, cocoa da zinare da ta yi fice a matsayinta na daya daga cikin kasuwanni mafi farin jini amma yanzu take fama da hauhawar farashi da wagegen gibin kasafin kudi.

Alkaluman hauhawar farashi sun kai kaso 15 cikin 100, a lokaci guda kuma darajar kudin kasar watau Cedi ta fadi da kusan kaso 30 cikin 100 idan an kwatanta da dala

Masu zanga-zangar, da yawansu sanye da jajayen riguna suna rera taken kin jinin gwamnati tare da bushe-bushe a lokacin da suke maci cikin lumana a kan titunan Accra, da rakiyar 'yan sanda.

Karin bayani