An dage dokar hana fita a Kaduna

Hakkin mallakar hoto KDGH
Image caption Gwamna Mukhtar Ramalan Yero na Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta dage dokar hana fita da ta saka a birnin Kaduna da kewaye sakamakon hare-haren bam da aka kai a jihar.

A ranar Laraba ne aka kai jerin hare-haren bam a garin Kaduna lamarin da ya tsaka al'umma cikin firgici da kuma zaman zullumi.

Sama da mutane 44 ne suka mutu a hare haren.

Hari na farko wanda aka kai a Alkali Road an kai shi ne ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi wani babban malami bayan da yake komawa gida daga bikin rufe Tafsir na azumi.

Na biyu kuma an kaddamar da shi a kan ayarin motocin Janar Muhammadu Buhari wanda ke fita daga garin Kaduna zuwa Daura.

Sheikh Dahiru Bauchi da Janar Buhari duk suna cikin koshin lafiya babu abinda ya same su.