'Yar Sudan da ta yi ridda ta koma Italiya

Batun Meriam Ibrahim ya janyo cece-kuce a duniya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Batun Meriam Ibrahim ya janyo cece-kuce a duniya

Matar nan 'yar Sudan wadda hukuncin kisan da aka yanke mata a kan zargin raddi, ya janyo martani a fadin duniya ta sauka a Italiya da Mijinta.

Babu wani karin bayani da aka bayar kan yadda hukumomi suka bar Meriam Yahia Ibrahim ta fice daga Sudan, amma dai ta samu rakiyar mataimakin ministan harkokin wajen Italiya.

An yanke wa Meriam Ibrahim hukuncin rataya saboda auren wani kirista, lamarin da hukumomin Sudan ke dauka a matsayin ridda ga mace Musulma.

A lokacin da take zaman jiran hukunci a gidan yari ne, Meriam Ibrahim ta haifi 'yarta jaririya.

Gwamnatin Sudan na daukar Meriam Ibrahim a matsayin musulma saboda shi ne addinin gidansu.