Jonathan ya gana da 'yan majalisar Nasarawa

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya gana da shugabannin majalisar dokokin jihar Nasarawa kan batun tsige gwamnan jihar, Umaru Tanko Al-makura da majalisar ke yunkurin yi.

Ganawar dai ta gudana ne cikin sirri a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Daya daga cikin 'yan majalisar ta jihar Nassarawa, Muhammad Okpede ya tabbatarwa BBC ganawar amma kuma basu tattauna shirin janyewa ko ci gaba da tsige Gwamna Al-Makura da Shugaba Jonathan ba.

A halin yanzu majalisar dokokin jihar ta Nasarawa da ke da jam'iyyar PDP ke da rinjaye, ta bayyana cewa babu gudu babu ja da baya a kokarin da suke yi na raba gwamna Al-makura da mukaminsa.

Alhaji Tanko Almakura dai shi ne gwamnan jam'iyyar adawa ta APC na biyu da ke fuskantar tsigewa daga mukamansa, bayan da aka tsige gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, a makon da ya gabata.

Karin bayani