An kafa kwamitin bincike kan harin bam a Kaduna

Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Muhammed Abubakar

Sifeta Janar na 'yan sandan Nigeria, Mohammed Abubakar ya kafa wani kwamitin bincike na musamman domin gano wadanda ke da alhakin kai hare-haren bam a Kaduna.

Lamarin ya janyo rasuwar mutane kusan 40 a Kaduna.

Sanarwar 'yan sandan ta ce kwamishinan sashin al'amuran shari'a ne zai jagoranci kwamitin wanda ya kunshi kwararrun jami'an bincike daga sassan rundunar daban-daban.

Hare-haren an kai su ne a kan tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari mai ritaya da kuma wani shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shiye-shiyen bukukuwar sallah a Najeriya, kuma zirga-zirga jama'a na karuwa a wannan lokacin.

Karin bayani